Malam Khalid.
Da fatan kana lafiya.
Na saurari wakokin Farfesa Sulaiman A. Tijjani guda uku. Na lura akwai wurare da ke neman gyaregyare kamar haka:
1. Wurare masu jan launi a cire su don babu su a cikin wakan.
2. Masu launin yellow kuma suna nuna duk inda muka yi yan gyara
saboda yanda na ji su a cikin wakokin.
3. Akwai kuma wurare wadanda na saurara a cikin wakokin amma ba a
rubuta su ba. Wadannan wuraren na nuna da asterisks (*****).
Takardar da muka yi gyara a kai za a tura maka.
A huta lafiya.
Dakta Bukar Usman
Daktan Adabi
Jagora: Dakta Bukar Usman Daktan Adabi
Ina Hindu ku zo mu gaishe shi
Dakta Bukar Usman Daktan Adabi,
Farfesa za na gaishe ka,
Kai wa }asa hidima
Ka kammala aikin gwamnati
Mun yi sam barka
‘Yan Amshi: Dakta Bukar Usman ka gawurta
Farfesa ya zo ya gaishe ka
Kai wa }asa hidima
Ka kammala aikin gwamnati
Mun yi sam barka
Jagora: Dakta Bukar Usman Daktan Adabi
Ina Hindu ku zo mu gaishe shi
‘Yan Amshi: Kai wa }asa hidima
Ka gawurta ga daktan adabi
A gaishe ka
Dakta Bukar Usman ka gawurta
Farfesa ne ke ta gaishe ka
Kai wa }asa hidima
Ka gawurta ga Daktan adabi
A gaishe ka
Jagora: Ya Ahadin Sarkin Sarakunna
Kai ke yin kyauta Kake }ari
‘Yan Amshi: Dakta Bukar Usman
Daktan Adabi
Farfesa ke ta gaishe ka
Jagora: Ba Ka da farau Kai ka fare ta
Farawa sannan ta sam fari
‘Yan Amshi: Kai wa }asa hidima
Ka kammala aikin gwamnati
Mun yi sambarka
Jagora: Al Ma’abudi ka]aitaka taka
Ga bautar ka ka samu kan tsari
‘Yan Amshi: Dakta Bukar Usman ka gawurta
Ya Allahu ya sanya albarka
Jagora: Al Hadi kuma kahhara taka
Rabbi muna ro}on ka albarka
‘Yan Amshi: Dakta Bukar Usman ka gawurta
Farfesa ya zo ya gaishe ka
Kai wa }asa hidima
Ka kammala aikin gwamnati
Mun yi sambarka
Jagora: Wandara ka aiko da Jakkada
Rahamatan a cikin halittunka
‘Yan Amshi: Dakta Bukar Usman
Daktan Adabi
Farfesa ke ta gaishe ka
Jagora: Sirril huda sayyidil kullul khairi
Gwanin barance gunka manzonka
‘Yan Amshi: Kai wa }asa hidima
Ka kammala aikin gwamnati
Mun yi sambarka
Jagora: Sallu ala Najamul huda kullu
Muhammadu da ya zo da sa}onka
‘Yan Amshi: Dakta Bukar Usman ka gawurta
Ya Allahu ya sanya albarka
Jagora: Wa ahlihi da sahabuhu jumlan Allah
Ka sa mu cikin masoyanka
‘Yan Amshi: Dakta Bukar Usman ka gawurta
Farfesa ya zo ya gaishe ka
Kai wa }asa hidima
Ka kammala aikin gwamnati
Mun yi sambarka
Jagora: Nan duniya in tayi ma shaida
Shaidar Allah ce a bayan ta
‘Yan Amshi: Dakta Bukar Usman
Daktan Adabi
Farfesa ke ta gaishe ka
Jagora: In ka ji gulbi ya ci mai ratsi
Sirri zan}am ne cikin batta
‘Yan Amshi: Kai wa }asa hidima
Ka kammala aikin gwamnati
Mun yi sambarka
Jagora: {irgin giwa babu buzunka
Bukkar daji ce a sunanta
‘Yan Amshi: Dakta Bukar Usman
Ka gawurta
Ya Allahu ya sanya albarka
Jagora: Dakta Bukar ka amsa sunanka
Gawurtacce babu tamkar ka
‘Yan Amshi: Dakta Bukar Usman ka gawurta
Farfesa ya zo ya gaishe ka
Kai wa }asa hidima
Ka kammala aikin gwamnati
Mun yi sambarka
Jagora: Mai kishin jama’a kamar Dakta
Na tai in nemo dukka na kasa
‘Yan Amshi: Dakta Bukar Usman
Daktan Adabi
Farfesa ke ta gaishe ka
Jagora: Ga gaskiya ga tsai akan aiki
Babu kasala sam a hannunsa
‘Yan Amshi: Kai wa }asa hidima
Ka kammala aikin gwamnati
Mun yi sambarka
Jagora: Al}alaminsa gidan azancinsa
Da hikima fikira da bun}asa
‘Yan Amshi: Dakta Bukar Usman
Ka gawurta
Ya Allahu ya sanya albarka
Jagora: Dakta Bukar ya zamma gamzaki
Baba su bar maka Rabbi ya ba ka
‘Yan Amshi: Dakta Bukar Usman ka gawurta
Farfesa ya zo ya gaishe ka
Kai wa }asa hidima
Ka kammala aikin gwamnati
Mun yi sambarka
Jagora: Wanda ya dau aiki tun daga fari
Har waladaina ya }ure aiki
‘Yan Amshi: Dakta Bukar Usman Daktan Adabi
Farfesa ke ta gaishe ka
Jagora: Tun a Clerk matsayinsa yaf fara
Har Permanent sec yai akan aiki
‘Yan Amshi: Kai wa }asa hidima
Ka kammala aikin gwamnati
Mun yi sambarka
Jagora: Duk mai son }arko akan aiki
Yay koyi da halin Bukar zaki
‘Yan Amshi: Dakta Bukar Usman
Ka gawurta
Ya Allahu ya sanya albarka
Jagora: Ka gagari mai }arya da mai suka
Dakta Bukar Allah ya fissheka
‘Yan Amshi: Dakta Bukar Usman ka gawurta
Farfesa ya zo ya gaishe ka
Kai wa }asa hidima
Ka kammala aikin gwamnati
Mun yi sambarka
Jagora: Farfesa in zan yi ma wa}a
Taka daban fasalin da zan rera
‘Yan Amshi: Dakta Bukar Usman
Daktan Adabi
Farfesa ke ta gaishe ka
Jagora: Yabon gwani ai ya zamo dole,
Gwalagwalen halin da kat tara
‘Yan Amshi: Kai wa }asa hidima
Ka kammala aikin gwamnati
Mun yi sambarka
Jagora: Ni da Bukar tamkar ma}era ce
Don gawayi ya sami mai }ira
‘Yan Amshi: Dakta Bukar Usman
Ka gawurta
Ya Allahu ya sanya albarka
Jagora: Ragwan amo shi ke bugun taiki
Mai wa}a Allahu ya baka
‘Yan Amshi
da Jagora: Dakta Bukar Usman ka gawurta
Farfesa ya zo ya gaishe ka
Kai wa }asa hidima
Ka kammala aikin gwamnati
Mun yi sambarka
********************
********************
Jagora: Domin darajar ilimi ta mai ilimi
Al Alimu Shi ya ke ba shi
‘Yan Amshi: Dakta Bukar Usman
Daktan Adabi
Farfesa ke ta gaishe ka
Jagora: Har ya zamo kogi fagen ilimi
Ka ji an ce babu tamkar shi
‘Yan Amshi: Kai wa }asa hidima
Ka kammala aikin gwamnati
Mun yi sambarka
Jagora: Shi ke da suttura da fahimta
Ba fahmi tamkar kamar na shi
‘Yan Amshi: Dakta Bukar Usman
Ka gawurta
Ya Allahu ya sanya albarka
Jagora: Ga shi Bukar Usman ya tumbatsa
Ai baiwar Allahu ba shakka
‘Yan Amshi: Dakta Bukar Usman ka gawurta
Farfesa ya zo ya gaishe ka
Kai wa }asa hidima
Ka kammala aikin gwamnati
Mun yi sambarka
Jagora: Ku sani Daktan nan ya burun}asa
Har a fagen Adabi ya zam Dakta
‘Yan Amshi
da Jagora: Dakta Bukar Usman
Daktan Adabi
Farfesa ke ta gaishe ka
********************
********************
Jagora: Domin kullun shi mafarkinsa
Ne duniyar adabi ta inganta
*********************
*********************
‘Yan Amshi: Kai wa }asa hidima
Ka kammala aikin gwamnati
Mun yi sambarka
Jagora: Arzikin shi da duk tunaninshi
Da duk tunaninsa ya al’umma za ta inganta
‘Yan Amshi: Dakta Bukar Usman
Ka gawurta
Ya Allahu ya sanya albarka
Jagora: Hamsha}i ka zamma limami
Dakta Bukar ilimi ya rene ka
‘Yan Amshi: Dakta Bukar Usman ka gawurta
Farfesa ya zo ya gaishe ka
Kai wa }asa hidima
Ka kammala aikin gwamnati
Mun yi sambarka
Jagora: Dakta Bukar ma}iyanka sun kasa
Sun gaji sun ce ka ri}e Allah
‘Yan Amshi: Dakta Bukar Usman
Daktan Adabi
Farfesa ke ta gaishe ka
Jagora: Shi mai }ulli in yana }ulli
Basshi da Allah kai ri}e Allah
‘Yan Amshi: Kai wa }asa hidima
Ka kammala aikin gwamnati
Mun yi sambarka
Jagora: Tasirin mai yin }ulunboto
Zai zo ne in ka sake Allah
‘Yan Amshi: Dakta Bukar Usman
Ka gawurta
Ya Allahu ya sanya albarka
Jagora: Dakta Bukar turare na almiski
Kyan halinka ya sa muke sonka
‘Yan Amshi: Dakta Bukar Usman ka gawurta
Farfesa ya zo ya gaishe ka
Kai wa }asa hidima
Ka kammala aikin gwamnati
Mun yi sambarka
Jagora: Malam Khalid kai ka hau layi
Don ka rabautu da falsafar Dakta
‘Yan Amshi: Dakta Bukar Usman
Daktan Adabi
Farfesa ke ta gaishe ka
Jagora: Sanda kana a magangarin
Tafki ambaliyarsa ko ka tsururuta
‘Yan Amshi: Kai wa }asa hidima
Ka kammala aikin gwamnati
Mun yi sambarka
Jagora: Al}alaminsa yana katantanwa
Haniniya don ga shi ga Dakta
‘Yan Amshi: Dakta Bukar Usman
Ka gawurta
Ya Allahu ya sanya albarka
Jagora: Khalid Imam Ala abokinka
Ya ce akwai fikira a salkarka
‘Yan Amshi: Dakta Bukar Usman ka gawurta
Farfesa ya zo ya gaishe ka
Kai wa }asa hidima
Ka kammala aikin gwamnati
Mun yi sambarka
Jagora: Wanda Bukar ya zamo mahanginsa
To zaya ]abbaku fal da banbanci
‘Yan Amshi: Dakta Bukar Usman
Daktan Adabi
Farfesa ke ta gaishe ka
Jagora: Shima tawari’u dai halin Dakta
Yay daurawa babu ninanci
‘Yan Amshi: Kai wa }asa hidima
Ka kammala aikin gwamnati
Mun yi sambarka
Jagora: Rumfar da tai fa]i ta }asaita
za ta yi ya]on innuwar ‘yanci
‘Yan Amshi: Dakta Bukar Usman
Ka gawurta
Ya Allahu ya sanya albarka
Jagora: Dakta Bukar Usman ka sau reshe
Khalid Imam ya ]au kamanninka
‘Yan Amshi: Dakta Bukar Usman ka gawurta
Farfesa ya zo ya gaishe ka
Kai wa }asa hidima
Ka kammala aikin gwamnati
Mun yi sambarka
*************************
*************************
Jagora: Khalid Imam sa}onka na mi}a
Na gaisuwa a gurin Bukar naka
‘Yan Amshi: Dakta Bukar Usman
Daktan Adabi
Farfesa ke ta gaishe ka
Jagora: Mai yin tsumi da halin Bukar Dakta
Zaren ka]i shine yake sa}a
‘Yan Amshi: Kai wa }asa hidima
Ka kammala aikin gwamnati
Mun yi sambarka
Jagora: Idan Bukar yay maka endorsing
Fagen rubutu wa kake shakka
‘Yan Amshi: Dakta Bukar Usman
Ka gawurta
Ya Allahu ya sanya albarka
Jagora: Dakta Bukar Khalid masoyinka
Amintakar nan ta yi albarka
‘Yan Amshi
da Jagora: Dakta Bukar Usman ka gawurta
Farfesa ya zo ya gaishe ka
Kai wa }asa hidima
Ka kammala aikin gwamnati
Mun yi sambarka
_
Wannan wa}ar Sulaiman A. Tijjani mai la}abin Farfesan Waka ya yi wa Dakta Bukar Usman a ranar Sha Uku ga Watan Satumba, 2015
Falsafa-Bukar Usman
Jagora: Ga mai falsafa abin koyi,
Ga mai falsafa ta alfarma,
Dakta Bukar yana da alkhairi,
Dakta Bukar yana da alfarma,
Dakta Bukar yana da alfarma.
‘Yan amshi: Tabbas ban yi zaton akwai kama tai ba.
Jagora: Ga mai falsafa abin koyi,
Mai kishin }asa da al’umma,
Dakta Bukar Usman Biu gamji,
Ban yi zaton akwai kama tai ba.
‘Yan amshi: Ga mai falsafa abin koyi,
Mai kishin }asa da al’umma,
Dakta Bukar Usman Biu gamji,
Ban yi zaton akwai kama tai ba. (2x)
Jagora: Dakta Bukar yana da alkunya,
Ga shi da kyautayi da alfarma
‘Yan amshi: Ban yi zaton akwai kama tai ba
Jagora: Sanin hakin mutum da ihsani,
Halin mutumtakarsa ya girma
‘Yan amshi: Shi Dakta Bukar ba ayi kushe ba
Jagora: Kishin }asa da gyra al’umma,
Ya zarce ka kira shi ingarma
‘Yan amshi: Mai falsafa ta gyara al’umma
Jagora: Gina mutum da taimakon na }asa,
Halin Bukar ba ayi kushe ba
‘Yan amshi: Ga mai falsafa abin koyi,
Mai kishin }asa da al’umma,
Dakta Bukar Usman Biu gamji,
Ban yi zaton akwai kama tai ba.
Jagora: Ga masanin tsaro akan tsari
Dakta Bukar yana da tsinkaya
‘Yan amshi: Ban yi zaton akwai kama tai ba
Jagora: In ka ga Dakta ransa ya ~aci,
To ha}}in mutum akan tauya
Amshi Shi Dakta Bukar ba a yi kushe ba
Jagora: Duk duniya tana ta kewarsa,
Halinsa ya rigaya ya raya
Yan amshi Mai falsafa ta gyara al’umma
Jagora: Da ayyukan }warai ka tumbatsa,
Za na fa]i, ba zan ji tsoro ba
‘Yan amshi: Ga mai falsafa abin koyi,
Mai kishin }asa da al’umma,
Dakta Bukar Usman Biu gamji,
Ban yi zaton akwai kama tai ba.
Jagora: Sonka da tallakawa bil Adama,
Gidauniyarka ga shi ta zauna
‘Yan amshi: Ban yi zaton akwai kama tai ba
Jagora: Gidauniyar Bukar Usumanu,
Ta daga darrajar mutane na
Amshi Shi Dakta Bukar ba a yi kushe ba
Jagora: Bukar taimako tunaninsa,
Don a hakan na san shi yay suna
Amshi Mai falsafa ta gyara al’umma
Jagora: Dakta Bukar Usman Biu ka,
Zama tauraron Najeriya Baba
‘Yan amshi: Ga mai falsafa abin koyi,
Mai kishin }asa da al’umma,
Dakta Bukar Usman Biu gamji,
Ban yi zaton akwai kama tai ba.
Jagora: Hadari kake mai ruwa na alkhairi
Dakta abin yabo a gun kowa
‘Yan amshi: Ban yi zaton akwai kama tai ba
Jagora: Ba son kai da nuna banbanci
Balle handama shirin wawa
‘Yan amshi: Shi Dakta Bukar ba ayi kushe ba
Jagora: {asar Biu ta yi da abin koyi
Najeriya ta sami dan baiwa
‘Yan amshi: Mai falsafa ta gyara al’umma
Jagora: Bukar ka rungume masoyanka
Su ma ma}iyanka ba su yi laifi ba
‘Yan amshi: Ga mai falsafa abin koyi,
Mai kishin }asa da al’umma,
Dakta Bukar Usman Biu gamji,
Ban yi zaton akwai kama tai ba.
Jagora: Mai }arfin gaskiya kamar zaki
Ka fi gaban mutum ya ce giwa
‘Yan amshi: Ban yi zaton akwai kama tai ba
Jagora: Amana kyan nufi da tsantseni
Su kan ‘yanta ]an Adam bawa
‘Yan amshi: Shi Dakta Bukar ba ayi kushe ba
Jagora: Kai aiki ka nuna }wazonka
Ka zama kai ake misaltawa
‘Yan amshi: Mai falsafa ta gyara al’umma
Jagora: Wanda ya ]auki falsafar Dakta
Bukar abadan ba zai yi }unci ba
‘Yan amshi: Ga mai falsafa abin koyi,
Mai kishin }asa da al’umma,
Dakta Bukar Usman Biu gamji,
Ban yi zaton akwai kama tai ba.
Jagora: Jama’a kukan rashin na mene ne
Muna da Bukar waye muke nema
‘Yan amshi: Ban yi zaton akwai kama tai ba
Jagora: Rumbun shawarar tsaro tari
CIA kwafa suke su ma
‘Yan amshi: Shi Dakta Bukar ba ayi kushe ba
Jagora: Shi ke article ta gawurta
Har ka ji duniya tana nema
‘Yan amshi: Mai falsafa ta gyara al’umma
Jagora: A nahiyar mu dukka na zaga
Dakta Bukar ban sam kamar shi ba
Yan amshi: Ga mai falsafa abin koyi,
Mai kishin }asa da al’umma,
Dakta Bukar Usman Biu gamji,
Ban yi zaton akwai kama tai ba.(2x)
Jagora: Haifaffen }asar Biu amma
Najeriya dukan yake kallo
‘Yan amshi: Ban yi zaton akwai kama tai ba
Jagora: Gudummawarsa ko ina har wasu
Kan fatan cikin su ya bullo
‘Yan amshi: Shi Dakta Bukar ba ayi kushe ba
Jagora: Inuwar gamjin Najeriya kwata
Shi fa]in duniya suke kallo
‘Yan amshi: Mai falsafa ta gyara al’umma
Jagora: Dan Usmanu ka ji sannu
Bukari kafin Ilahuna Rabba
‘Yan amshi: Ga mai falsafa abin koyi,
Mai kishin }asa da al’umma,
Dakta Bukar Usman Biu gamji,
Ban yi zaton akwai kama tai ba.
Jagora: Marigayiya Allahu ya jikanta
matarka ce Bukar ta alfarma
‘Yan amshi: Ban yi zaton akwai kama tai ba
Jagora: Kemi ta san mutunta al’umma
Duka halinka sun sani su ma
Mutuwa ya kike mana shigar sauri
Har kika wa Bukar bugun dama
Allah ya kau da kansa a gare ki
Uwargidan Bukar farin duba
‘Yan amshi: Ga mai falsafa abin koyi,
Mai kishin }asa da al’umma,
Dakta Bukar Usman Biu gamji,
Ban yi zaton akwai kama tai ba
Jagora: Sarauniya sarauniyar mata
Dupe zuwanki ya yi alkhairi
‘Yan amshi: Ban yi zaton akwai kama tai ba
Jagora: Matar Bukar daban cikin mata
Sai ku biyo ta don ku ]au tsari
‘Yan amshi: Shi Dakta Bukar ba ayi kushe ba
Jagora: Mai nattsuwa da babu inkari
Uwarmu ga uwa ]ibar fari
‘Yan amshi: Mai falsafa ta gyara al’umma
Jagora: Dupe matar Bukar Usmanu
Kin gyara Bukar da kyan duba
‘Yan amshi: Ga mai falsafa abin koyi,
Mai kishin }asa da al’umma,
Dakta Bukar Usman Biu gamji,
Ban yi zaton akwai kama tai ba.
Jagora: Dakta Bukar ga gaisuwar girma
‘Ya’yanka ma baza na manta ba
‘Yan amshi: Ban yi zaton akwai kama tai ba
Jagora: Halimatu Halima Sa’adiyya
Khadija kun biyo halin baba
‘Yan amshi: Shi Dakta Bukar ba ayi kushe ba
Jagora: Kyawun ]a ya gaji babansa
Hafsatu ma baza na manta ba
‘Yan amshi: Mai falsafa ta gyara al’umma
Jagora: Mairo da Fatima Allah jikansu
Kai rahama gare su ya Rabba
‘Yan amshi: Ga mai falsafa abin koyi,
Mai kishin }asa da al’umma,
Dakta Bukar Usman Biu gamji,
Ban yi zaton akwai kama tai ba.
Jagora: Ke ma Zahra’u sannu sannunki
Ke ma za ki samu tarbiyya
‘Yan amshi: Ban yi zaton akwai kama tai ba
Jagora: Duk wanda Bukar ya zamma babansa
Zai zama alfijir ga dubayya
‘Yan amshi: Shi Dakta Bukar ba ayi kushe ba
Jagora: ‘Ya’yan Bukar suna da tarbiyya
Neman ilimi ku kara lun}aya
‘Yan amshi: Mai falsafa ta gyara al’umma
Jagora: Dakta Bukar shi ne katafare
Ban yi zaton akwai kama tai ba
‘Yan amshi: Ga mai falsafa abin koyi,
Mai kishin }asa da al’umma,
Dakta Bukar Usman Biu gamji,
Ban yi zaton akwai kama tai ba.
Jagora: Farfesan waka wakar }arni
Ban ]ara ‘yan uwa azanci ba
‘Yan amshi: Ban yi zaton akwai kama tai ba
Jagora: Wa}ar Bukar nake cikin shau}i
Kamar ba za na kai ta karshe ba
Yan amshi: Shi Dakta Bukar ba ayi kushe ba
Jagora: Babu tsumi bani da dabara
Farfesa bawanka ne Rabba
‘Yan amshi: Mai falsafa ta gyara al’umma
Jagora: Hindu ki zo ki amsa waken nan
Fagen wa}ar wace ce ba ke ba
‘Yan amshi: Ga mai falsafa abin koyi,
Mai kishin }asa da al’umma,
Dakta Bukar Usman Biu gamji,
Ban yi zaton akwai kama tai ba.
Jagora: Dakta Bukar yana da alfarma
Dakta Bukar yana da alfarma
Dakta Bukar yana da alfarma
Dakta Bukar yana da alfarma
‘Yan amshi: Tabbas ban yi zaton akwai kama tai ba.
Jagora: Ga mai falsafa abin koyi,
Mai kishin }asa da al’umma,
Dakta Bukar Usman Biu gamji,
Ban yi zaton akwai kama tai ba.
‘Yan amshi: Tabbas ban yi zaton akwai kama tai ba.
_
Wannan wa}ar Sulaiman A. Tijjani mai la}abin Farfesan Waka ya yi wa Dakta Bukar Usman a ranar Goma ga Watan Satumba, 2015
Garnakaki-Dakta Bukar Usman
Jagora: In ka ]ara shi tarin dukiya,
Shi ya ]ara ka tarin arziki
In ka ]ara shi tarin shekaru,
Hankali ba za a daidaita ku ba
Sunan da ya yi kai ba ka yi shi ba,
In ko ka yi shi to da akwai wata
Gangaran fage na fannin ilimi,
Mai ja da shi, ku ban wani ko wata
In ko ka fi shi tarin ilimi,
Kogin sani akwai fa]i haka
Duniya ta yin rubutu ya sano,
Kuma littafan tulin dalar-zuru
In ka ]ara shi tarin littafai,
To nan gurin ba za ko ka tsira ba
Shaida akan Bukar Usman Biu,
Ta saka ya zama Daktan adabi
Garna}a}i Bukar Usman Biu,
Mai ilmi da aiki na} }warai,
Bangon gabas sani tamkar ruwa,
Kai mamaya Bukar Usman Biu
‘Yan amshi: Garna}a}i Bukar Usman Biu,
Mai ilimi da aiki na} }warai,
Bangon gabas sani tamkar ruwa,
Kai mamaya Bukar Usman Biu (2x)
Jagora: Shi yin yabo bawa nag gari,
Mai yi ba za a muzanta shi ba
Da gwala-gwalan kalamai don aji,
Kunne ba sa wula}anta su ba
Murya da kambami na amon batu,
Zuciya ba ta }i kwarzanta su ba
Na zo da wata wa}a sabuwa,
Zan zayyano Bukar Usman Biu
‘Yan amshi: Garna}a}i Bukar Usman Biu,
Mai ilimi da aiki na} }warai,
Bangon gabas sani tamkar ruwa,
Kai mamaya Bukar Usman Biu
Jagora: Mai ilimi amanar ilimi,
Sha tambaya Bukar Usman Biu
Ga shakwaraniya tilon mutum,
{arfen diga Bukar Usman Biu
Fannin adab da harkar ilimi,
Najeriya tana a garin Biu
Adabi yana maraici ba uba,
Sai ga zuwan Bukar Usman Biu
‘Yan amshi: Garna}a}i Bukar Usman Biu,
Mai ilimi da aiki na} }warai,
Bangon gabas sani tamkar ruwa,
Kai mamaya Bukar Usman Biu
Jagora: Dattijo mai abin al’ajabi,
Ga fikira da baiwar hattara
Allahu in yana kyautarsa shi,
Za~insa shi yake baya jira
Mai yin tasarrafi na ruwan sama,
A cikin ruwa ya wassafa }an}ara
Kogin sani idan ya makaro,
Bayansa kwai Bukar Usman Biu
‘Yan amshi: Garna}a}i Bukar Usman Biu,
Mai ilimi da aiki na} }warai,
Bangon gabas sani tamkar ruwa,
Kai mamaya Bukar Usman Biu
Jagora: Shi Bukar yana da kaifin hankali,
Hange na nesa ko ba a kai shi ba
Ga }o}ari na neman arziki,
Experience Bukar ba baya ba,
An yo gwagwarmaya an sha wuya,
Neman halaliya ba }ware ba,
Fa]in }asar ga ba sai gobe ba,
Ba mai kamar Bukar Usman Biu
‘Yan amshi: Garna}a}i Bukar Usman Biu,
Mai ilimi da aiki na} }warai,
Bangon gabas sani tamkar ruwa,
Kai mamaya Bukar Usman Biu
Jagora: Jarumin mutum da ba shi da fargaba,
Tsoro yana gudun kai turjiya,
Ga tausayi da kawo ci gaba,
Zuciyarsa ce irin ta mazan jiya,
Mai nattsuwa da kyawun lafazi,
Halinsa bai hali na wahainiya,
Daktan adab Bukar Usman Biu,
Ha}uri da shi ku ce musu ‘yanbiyu
‘Yan amshi: Garna}a}i Bukar Usman Biu,
Mai ilimi da aiki na} }warai,
Bangon gabas sani tamkar ruwa,
Kai mamaya Bukar Usman Biu
Jagora Kyauta zubar ruwa takwaransa ne,
Hannunsa bu]e ba wai ruffe ba,
Sannan akwai ibada ko’ina,
Ba dai yayo nufinka da aibu ba,
Rana kake Bukar Usman Biu,
Hannu ba zai hijabance ka ba,
In Rabbi ya nufe ka da arziki,
Koyi ka ]au Bukar Usman Biu
‘Yan amshi: Garna}a}i Bukar Usman Biu,
Mai ilimi da aiki na} }warai,
Bangon gabas sani tamkar ruwa,
Kai mamaya Bukar Usman Biu
Jagora O.O.N babbar lambar yabo,
An ba ka sanadin jajirtuwa
Shi ]an halas ake wa hasafi,
In ya ishe ku ba ya mantuwa
Lardin }abilukan Najeriya,
Fata suke ina suyi tsuntuwa
[anyan lu’ilu’i na }asar Biu,
Babban mutum Bukar Usman Biu
‘Yan amshi: Garna}a}i Bukar Usman Biu,
Mai ilimi da aiki na} }warai,
Bangon gabas sani tamkar ruwa,
Kai mamaya Bukar Usman Biu
Jagora Ya zaga duniya ta san da shi,
Al’adu kan shi bai manta su ba,
Babban sakatare ne ko a da,
Lambar yabo ba ka }irga su ba,
Ya tara ilimi ma}il aka,
A fage na yin rubutu ya zuba,
Mai son Rasulu ya gama arziki,
Allah idar Bukar Usman Biu
‘Yan amshi: Garna}a}i Bukar Usman Biu,
Mai ilimi da aiki na} }warai,
Bangon gabas sani tamkar ruwa,
Kai mamaya Bukar Usman Biu
Jagora Gudunmawarka ba ta }irguwa,
Nan duniya a fannin ci gaba
Fasalilluka na fannin ilimi,
In ka tabo shi sai ka ji ya iya,
Duk jami’ar da ke Najeriya,
Ta karrama shi domin ya iya,
Raba gardaman sani duka nahiya,
Amsarmu ne Bukar Usman Biu
‘Yan amshi: Garna}a}i Bukar Usman Biu,
Mai ilimi da aiki na} }warai,
Bangon gabas sani tamkar ruwa,
Kai mamaya Bukar Usman Biu
Jagora Ka rayu da iyaye lafiya,
Ga ‘yan’uwa su nai maka godiya,
Dakta Bukar ka gode Rabbana,
Kanzul ilim ya sa maka ajjiya,
Majiya kishi a fannin ilimi,
Ga Bukar mu je mu kurba maliya,
Baiti nake zabainar zantuka,
Kai mamaya Bukar Usman Biu
‘Yan amshi: Garna}a}i Bukar Usman Biu,
Mai ilimi da aiki na} }warai,
Bangon gabas sani tamkar ruwa,
Kai mamaya Bukar Usman Biu
Jagora {ungiyar adabin gargajiya,
Sun karrama ka baba mu je zuwa,
Kungiyar masana kan harsuna,
Najeriya da Nijar ‘yanuwa,
Sun zo da jinjina sun jinjina,
Sun karrama ka Dakta garkuwa,
Sun yo yabo gami da gudunmawa,
Sai godiya Bukar Usman Biu
‘Yan amshi: Garna}a}i Bukar Usman Biu,
Mai ilimi da aiki na} }warai,
Bangon gabas sani tamkar ruwa,
Kai mamaya Bukar Usman Biu
Jagora Farfesa Abubakar Adam Rashid,
VC na Bayero yay jinjina,
Farfesa Salisu ]an Fodiyo,
Yakasai ya nai maka jinjina,
Ga jami’ar Kaduna State ha]e,
Farfesa Babajo yay magana,
Farfesa Bello Sa’id daga Bayero,
Duk sun yabon Bukar Usman Biu
‘Yan amshi: Garna}a}i Bukar Usman Biu,
Mai ilimi da aiki na} }warai,
Bangon gabas sani tamkar ruwa,
Kai mamaya Bukar Usman Biu
Jagora Farfesa Ibrahim Malumfashi,
Daga Jami’ar Kaduna yana yabo,
Farfesa Sani Abba na A.B.U,
Shi ma Bukar yana mi}o yabo,
Farfesa Abdu Yahya Bichi,
Ahalin abin bisa babban rabo,
Mai halin }warai Bukar Usman Biu,
Mai cibiya a binne }asar Biu
‘Yan amshi: Garna}a}i Bukar Usman Biu,
Mai ilimi da aiki na} }warai,
Bangon gabas sani tamkar ruwa,
Kai mamaya Bukar Usman Biu
Jagora To ku dakata akwai wani ]an batu,
Tafkin kada mutum ba ya shiga,
Don na ji gangaran ya jinjina,
Madatsar sani ba ai mata marraga,
{ofa ta ilimi kakanmu ne,
Dajin sani ta gunka ake shiga,
Farfesa gangaran [andatti ne,
Ya zo da jinjina ga Bukar Biu
‘Yan amshi: Garna}a}i Bukar Usman Biu,
Mai ilimi da aiki na} }warai,
Bangon gabas sani tamkar ruwa,
Kai mamaya Bukar Usman Biu
Jagora Alhaji Salisu Na’inna farin mutum,
A wajen Bukar ba ai maka kore ba,
M.O.N Ado Ahmadu ]a,
Mai Gidan Dabino ban manta ka ba,
Malam Khalid Imam na gurinka ne,
Dakta Bukar ba zai }i yabonka ba
Riga ta martaba ga kwarjini,
Suttura Ilahu yayi wa Bukar Biu
‘Yan amshi: Garna}a}i Bukar Usman Biu,
Mai ilimi da aiki na} }warai,
Bangon gabas sani tamkar ruwa,
Kai mamaya Bukar Usman Biu
Jagora Sai godiya a gunka Ilahuna,
Da na yo arangama da farar zuma,
Sanadin za}a}uri Khalid Imam,
Littafan Bukar ya zam na kankama,
Zan yo aman adab da na daddaka,
Khalid Imam ya ce nai azzama,
Taskar Tatsuniyoyin Hausawa,
Daga littafan Bukar Usman Biu
‘Yan amshi: Garna}a}i Bukar Usman Biu,
Mai ilimi da aiki na} }warai,
Bangon gabas sani tamkar ruwa,
Kai mamaya Bukar Usman Biu
Jagora A fagen batu na wa}ar zamani,
Na san akwai maza ban bara ba,
Farfesan wa}a ]an Paki ne,
Ambaliyar amo ba baya ba
Dakwarar dafi ]agawar zamani,
[anmagori ]amararsa ba zan yi ba,
Da ma}ogwaro nake buga littafa,
Kan rayuwar Bukar Usman Biu
‘Yan amshi
da jagora: Garna}a}i Bukar Usman Biu,
Mai ilimi da aiki na} }warai,
Bangon gabas sani tamkar ruwa,
Kai mamaya Bukar Usman Biu (2x)
_
Wannan wa}ar Sulaiman A. Tijjani mai la}abin Farfesan Waka ya yi wa Dakta Bukar Usman a ranar Biyu ga Watan Satumba, 2015
Tarihin Sulaiman Farfesan Wa}a
Cikakken sunansa shi ne Sulaiman A. Tijjani. An haife shi a ranar litinin 12 ga watan Disamba, shekara 1983, a garin Paki cikin }aramar hukumar Ikara da ke jihar Kaduna. Ya fara karatun Firamare a mahaifarsa ta garin Paki, daga nan a ka tafi da shi Fulatan da ke }aramar hukumar Rogo ta jihar Kano. Bayan ya kammala firamare, sai ya tafi makarantar koyon karatun addinin musulunci wato karatun allo. Bayan kimanin shekaru biyar, Sulaiman ya dawo domin ]orawa daga inda ya tsaya a karatun zamani. Ya ci gaba da karatunsa a babbar sakandaren gwamnati da ke garin Paki, watau GSS Paki, ya kuma kammala a 2010. Sulaiman ya tsunduma a harkar wa}a cikin shekarar 2011. Har zuwa yanzu yana kan neman karatu. Yanzu yana da shekaru 32. Ya samo la}abin Farfesa ne saboda tun yana }arami ba shi da burin da ya wuce yin karatu har ya kai mataki na zama farfesa. Don haka ake masa la}abi da wannan suna.
No comments:
Post a Comment