Saturday, 19 March 2016

BAWAN ZUCIYA

9-08-2015.
BAWAN ZUCIYA
Shimfida:
Farfesa sai ka bi a hankali
Son zuciya bacin zuciya
A rayuwa sai ka bi a hankali
Farfesa na ce kab bi a hankali
Son zuciya wani bacin zuciya
Gadar zare yin gadon tumfafiya.

Ga wata waka bawan zuciya Hindu ki zo ayi wakar nan da ke
Farfesa sai ka bi a hankali ko ko ka zam bawan son zuciya.
Gantali ko yawon sharholiya Gadar zare mai girke rijiya a rayuwa sai ka bi a hankali ko ko ka zam bawan son zuciya.
1
Ka kaddara kayanka su na cikin jaka ta mai tafiya ka rataya,
Ka zo kadar raba wata nahiya ba 'yar sanayya ko da ka zagaya,
A hankali hakuri karyar rabo kwana kadan sunanka ya kewaya,
Shi kenan ka koma dangari sai ka shagaltu da neman dukiya
2
A zuciya da akwai wani ba'ari shi ke da hakkin tsarkake zuciya,
Hannu guda 'yan girka gadar zare su na ta faman girke rijiya,
Gaba dubu in ka zurma ka mula a duniya ka koma mujiya,
Hali guda hudu in ba ka bar su ba za ka dade a cikin hauragiya.
3
Hali na tsoro halin dan kare; dan kuikuyo don ba shi da zuciya,
Halin biri barna mamugunciya ga bai da tsoron mai ma sa tarbiya,
Kaya niki tafiyarsa da kyar da kyar ga littafa da tulin kin gaskiya,
Tururuwa hadama ga handama ba ta gudun wani bacin zuciya
4
Duniya dauke ni a hankali ki je da ni ki aje ni a hankali,
Domin idanki guda ne tal a ka kar ki aje ni a gefen cokali,
Kwaranniya mai rai ba ta bar ka ba na ruwa bai wa kadoji izgili,
A rayuwa sai ka bi a hankali ko ko ka zam bawan son zuciya.
5
Allah Ka mai da mafarki zahiri ran tahmidi ranar za'ida,
Lumbau rabon kwado na nan a kas diyar barewa ta fi diyar gada,
Badon cikin ruwa ban bashe shi ba abin a killance ne ko a da,
Farfesan waka luguden batu arangamar yaro bisa tukkuba.
6
Ga waka sabanin hankali in hankali bai kai nisanta ba,
Azarbabi na biyewa zuciya mutum ka lura ba zai fisshe ka ba,
Idan ka bi ta da so ta kada kai domin ka na bautar mara martaba,
 Son zuciya ne bacin zuciya madindimi a cikin barababiya.

Farfesan waka

No comments:

Post a Comment