Sunday, 20 March 2016

HAWAYEN ZUCI farfesan waka

18-05-2015

HAWAYEN ZUCI

Da hawayen zuci da sani barancen kura
Da hawayen zuci da-na-sani sanin wasu bayi.

Da hawayen zuci da-na-sani kwantancen kurma.

1
Da hawayen zuci mai gaddama ya kan bar kowa,
Hadarin tsantseni kar kai gudun gujewa kowa,
Nasarar dan sarki yay rayuwar da babu dagawa,
Ganga tai zaki da barazana katsowar giwa,
Illar yin karya bajima dade ta na saka shayi.
2
Da hawayen zuci a gurin Ilahu nai mafakana,
Bani tsoron bacci kwanciyar da zan yi ne damana,
Sauna ko gaula shi ke zama na dannin zana,
Da walakin lallai ga dan fatsar ya na kin tana,
Bayan kololi jifa zai sauka babu majanyi.
3
Bari yin zanbarma zuciya tilas na yi miki tufka,
In ga karafka to madugu ake wa turaka,
Da hawayen zuci mai nakuda ta ke yin kuka,
Ya na gawar shanu in kai jira jiran molanka,
Na san za a rina satar zanan bugawar sanyi.
4
Zuciya tai nauyi ga zantuka cikin kirjina,
Duk jiki sai kyarma don na ji an kira sunana,
Waiwaye nai baya gaba na zaka ta babu wanina,
Dandazon 'yan gwalalo mujiyoyi ke dara a gidana,
Zullumi ya bijiro kila nai gamon miyagun bayi.
5
Ga dare ya tsala ga walkiya alamu na ruwa,
A cikin dakina zumbur na tashi babu sakewa,
A dama kansakali a hagun da fitilata ta ruwa,
Da farin gwado yafe haka naz zaka wajen ba kowa,
Farfesan wake a cikin rashin sanin me zan yi.

Farfesan waka
20-0302016

No comments:

Post a Comment