11-08-2015
BIKO
Biko neman gyara mai taguwa ya gagari mai koma
- ya ku ka ce
A labarin biko Farfesa da zance bakinka
1
Na tashi ina kuka da hankacif na share goshina,
Abin ya doke ni ga zuciya ta na faman kuna,
A cikin mota naz zo na kasa waiwaye ko in zauna,
Hawaye sun tsatso na bata dukka sashin rigana,
Kai da sauran labari mai rai abin ka zo kai min kuka.
2
Gidana kwai fadi da na shigo ciki yay min tsuku,
Kafin na wuce aiki abinci zan dafa shi irin na ku,
Da zarar na na dawo me zan yi kan na huta a zatonku,
Shara domin tsafta ni zan yi tunda ba ni da ko kuku,
Cikin wancan dangi akwai mutum da ke kan hana yin kuka
3
Na je gun mamana uwa garen da tsantsar kaunata,
Na kwashe labari na ba ta hankali ya ragaita,
Ta dan dafo kaina ta ce na je komai zai daidaita,
Don komai ya dame na rasa yadda zan yi na inganta,
Dare ko ko rana na shiga tasku sai faman kuka
4
Na yarda da laifina na daina dora laifin kan kowa,
Zuciya ta damfaru ni dai garen ku ce turken wawa,
Sutturarka ta na gunka abokanan zama bari gaugawa,
Da zaman ba tangarda halin mutum ya ke ja mar tsawa,
A labarin biko na sha wiya gurin wancananka.
5
A gurin aiki zafi cikin gida da hanya ba dadi,
Aminci riga ne idan a kai wa juna kwai dadi,
Biko neman gyara a hakurewa juna kwai dadi,
Zato aikin banza ko yay gamon-katar sai an fadi,
Abinda da a kai baya a gaskata ni kar da sa sahakka
Farfesan waka
07-01-2015
No comments:
Post a Comment