Friday, 16 December 2022

22-03-2016
YAHANASU
Ga wata gimbiya kamar sarki,
Mai ado da alfarma,
Arziki da bunkasa,
Dukiya tili baiwa,
Ba ta gaji tsoro ba,
Jarumtaka kamar sarki,
Kyauta ta ke a na kuka,
kyatatawa Talakawa,
Kwarjini kamar giwa,
Ilimi da addini,
Martaba ta tsinkaya,
Ga Farfesan waka naz zo,
Farfesan waka naz zo
Don na wake yar sarki,
Alkebba gurin mata,
Allah ya kara alfarma.

Tamburanki ne giwa kankada fashe koma
Hajiya Yahanasu taka a sannu 'yar Sarki
Alkebba adon mata duk gimbiya ba tai ke ba
1
Allah Huwallazi Wanda ya kagi mai farke yay bacci,
Ya yo zakakurai da ibada su ke gudun bacci,
Ya za ku kaddara kai daya za su yo da mai bacci,
Mai dajiya da lilon karfe bai san katsewa ba.
2
Tsira gami da dukka aminci ga Annabin kowa,
Najamul huda Mubasshir Rahmar izo gidan kowa,
Da ahlihinsa har asahabu makwaikwayar kowa,
Da Sulaiman da ban wake gimbiya kamar ke ba.
3
Hajiya Yahanasu mai takama da son Allah,
Komai tsawon dare ba ta daina bi da yin sallah,
Kwana ta ke ibadar Allah ta na kiran Allah,
Wane mutum ko ta zam gamji ba ta ki tofo ba.
4
Gimbiya ki ke yar sarki da babu tamkar ke,
Mai ayyukan kwarai mai hakurin da babu tamkar ke,
Kyauta kamar ruwa yanzu a ba ka a dada sai ke,
Gimbiya Yahansu ga gimbiya farar duba.
5
'ya 'yan sarakuna duk duniya ke ce su ke kallo,
Ke ce diyar iyakar mulki batunjumin kallo,
Mai martaba uban talakawa gaji mai kallo,
Dan Abdu mai dashen adalci Allah jikan baba.
6
Tilas a yau na yo kuka na tuna da babana,
Tilas a yau na yo kuka na tuna da babana,
San Kano jinin Bayero ka ji mai dishe rana,
Mutuwa kin rushe bango majiginar duba.
7
Mulki da kwarjini da muhibba ba ai kamar shi ba,
Khadimi na addini walittaka farin duba,
Kasaituwa da dinbun baiwa ba zan kwatanta ba,
Waliyyin sarakuna Takawa ba ai kamar shi ba.
8
Allah kara yin bajakolin jinkai ga mai girma,
Alh sarki Ado dan Bayero mazan fama,
Toronge takamar duk sarki ya zo da bangirma,
Allah Ka dauke kai kan duk kuskuren farin duba.
9
Kamar uwa  kamar danta ba cinkaro a zancena,
Gimbiya Yahanasu ke ce tsatso tsiron gona,
Kowa ya hangi 'yar sarki zatinsa zai ga kin nuna,
Taka a lafiya dutsen ruwa bai san da rana ba.
10
Sifa, zubi da kasaita da ke ce ki ke kamar sarki,
Dirkar sarakuna Ado dan Abdu ne madon sarki,
Kyauta da kyautaye kin rikide halin mahaifinki,
Dawisu jinjina 'ya 'yan sarakuna ba ai ke ba.
11
Basarakiya ki ke tumbatsarki ta fi wani sarki,
Domin jininki ya dau nasaba ku na gidan zaki,
Babu 'yar burun-burun babu tawai babe akan doki,
Gimbiya kamar tauye gadon da ba ki gada ba.
12
Karyar makwangwara kin zama ginshiki diyar girma,
Wataran da mai gida zai tafiya ki kai Shiri ke ma,
Wasu na taraliyar kulla shirin cire rubin dama,
'yar lelen san Kano England kun ka tai da ba wai ba.
13
Gimbiya Yahansu tauraronki na disashe su,
Matsayi abin nufi Allah ne ya ba ki ba su kyale su,
Lu'lu'i zubarjadu da kamala ta mai tagwan masu,
Gimbiya Yahanasu Allah ya yi ki ba wai ba
14
Zan gaisuwa gurin 'ya'yan gimbiya diyar sarki,
Zan gaisuwa Halifa jikan gidan sarki,
Tilas na zo na gaida Taheera jikar gidan sarki,
Sajeed ina kake dan baiwa jikan gidan sarki,
Ina Bilalu dan Giimbiya jikan gidan sarki,
Ga gaisuwa gurin Saddika jikar gidan sarki,
'ya'yanki ne na ke gaishe su gimbiyar sarki,
Hajiya Yahanasu jinin girma diyar farin duba.
15

Ga ki gimbiya alfarma ga bin mijin  aure,
Mata na yanzu ga wacca ta fi ku gane bin aure,
 Gado na hankali da biyayya ta zo gidan aure,
Ga mijinta karshen girma bai gaji wasa ba
16
Namijin duniya Abdulmalik bai san da kyashi ba,
Ga gaskiya riko na amana bai san mugunta ba,
Ga kokari da sada zumunci ba mai fada ne ba,
Neman na kansa kullun ya sani bai kalli kowa ba.
17
Yaya Sa'ida sannu ki dai ba za na manta ba,
Na mika gaisuwar ban girma ba kya ki karba ba,
Kane ga gimbiya sannu Zubairu ba rago ne ba,
Gimbiya Yahanasu ga 'yan uwanki ba wai ba
18
Kyawun diya ta gaji mahaifanta kun ga tai riba,
Sannu mama Hajiya Zainab diyarki tai haiba,
A gurinki ne ta dau tarbiyar da ba ta watsar ba,
Gimbiya Yahanasu ta dau halinku tai riba
19
Hajiya Zainaba sam ba ta dauki duniya can ba,
Jikanki ne Sulaimanu ya zo da gaisuwar hubba,
Kin haifi zinare ko ko zinariya da ba wai ba,
Tuyar da albasa ta bace ba za a sami kamshi ba

Farfesan waka
25-03-2016

No comments:

Post a Comment