Saturday, 16 April 2016

A CAPTIVE NOW OUTCAST

CAPTIVE NOW OUTCAST

Oh! A solitary mother
Or a misfortune lad
I passed through
Many hard moments;
That scattered the memory
And shattered the history
Hardly one erase
As inscriptions surfaced a stone
Boiling in me.

Newly introduced disaster
Into the hand we fell victims
Happened in a reverie but
True and not pen-peeling
Crafting either

I remember when and how
All were darting for escape
But all of no avail
Chasing in daring
Mothers throwing children
Children vacanting the arms
Like herder and animals
Both escaping the destroyed farm
Owner

Terrible wind swayed the peace
Living society
Now a war-like village
Skirts and trousers
Amidst the epidemic nighmare
Sky echoed the mixture
Of melancholy
Constantly flooding
The poor ears
Madly in fright
I ran through the swirling dust
All splashed with mud
And blood took over
The sight
The effort defeatedly in vain

Women all in tattered cloth
Disorganized by fear
And terribly unkempt
Herded up like cows
No!
Beyond
For the herdsman leads
Guides and protects
To home or a river of green bank

The men were finished
The invaders happily celebrating
The victory
Were we captives?
Two before us to take either
Marriage or booty?
Former would do
If all one must do

Captives tested more
Slavery in multiples
Oh! Some went through number
Of rapes mercilessly,
Everyday not a day
Crying through night losing hope
In the day

They massacred yesterday
Today defeated and cleared
We are to home again
In me unwanted seed
What a nostalgia!
I finally made a fruit
Unwanted?

Society didn't accept me
Family too
What will be
Of both ill-fated mother
And the destined child
I stood for all
Love foolishly kept me
Fit for the blame

Seventeen old in dilema
A captive now an outcast
And I love the child.
By
 FARFESAN WAKA




Monday, 11 April 2016

GARIN BIU farfesan waka

GARIN BIU

Yar Amshi:
Farfesan waka himma haka dai,
Jagora:
SHIMFIDA
Yankin gabas mu na da garin da ya fi saura,
Gagarimin garin da ba za a ja da shi ba,
Hauragiyar macuta ba ta mar dabaibayi ba,
Shi ne garin da sam bai san da faduwa ba,
Shi ne garin da 'yan gangan ba za su je ba,
Shi ne garin da annoba ta sallama wa,
Shi ne garin da tarihi ya kawwamewa,
Shi ne garin da alfarma ta kambama shi,
Shi ne garin jarumta ta jinjina wa,
Karni aru-aru aka san shi ya yi suna,
Shi ne gari saman tsauni da masarauta,
Shi ne garin yay shura fagen dabara,
Shi ne garin da fintinkau ya ke wa saura,
Shi ne garin da kyan yanayi ba ko kama tai,
Shi faskaren gwani hadda ke sa a wanke,
Binkice matakala mai kai mutum ga turke,
A duniya gari uku sun ka ba shi rata,
Ina nufin gari uku ne su ke gaba nai,
Kololuwar batu harshe ba zai fada ba,
Garin ga ya wuce zancen da zan fada ma,
Na tausaya ga wanda idansa bai gani ba.
Amshin Jagora:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa, ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba Farfesa na ce ba ka zaga ko'ina ba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa, ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
'Yar Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa, ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba Farfesa na ce ba ka je garin gani ba.
1
Ya Al-Ahdu Mai suna gaban kidaya
Gata ga mai uwa da uba gatan maraya
Jinbantake ni Allahna na bar karaya
Na dinga baituka ban cimma faduwa ba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
2
Tafkin da ke gaji da maji kishi da baiwa
Haske madawwami Ni'ima gusar da rowa
Da ahlihi hada da sahabu hadimaawa
Rasulun Mubasshirin wa zai yi ba da kai ba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
3
Wanda duk ya zagaya jamhuriyar kasata,
Daga maghrib ya je izuwa gabas mabauta,
Arewa da dak kudu ya bar Biu a manufata,
To sai na ce da shi bai je garin gani ba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
4
Garin maraba bako gun da ba mugunta,
Babban gari Biu am mas shaidar nagarta,
Garin da illimi ke wa ayyukansu gata,
Hamshakin gari ba a kai shi arziki ba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
5
Shi ne garin da yaki bai rugurguza ba,
Ko kwana dubu a ke artabu ba da wai ba,
Su ke da garkuwar da ba za a tunkude ba,
Tarihin garin Biu masana su ke wa duba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
6
Zakakuran barade ba su ja da baya,
Garin Biu nan turawa su ke wa gayya,
Amma su kai zugum sun kasa masa kawanya,
Gari gaban gari Biu za ka je ka duba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
7
Kuma tun katin-katin da ake ta tallatawa,
Sun kai riko da addini da girmamawa,
Domin idan da yaki za su sallamawa,
Jama'ar Mujaddadi ba za su dangana ba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
8
Garuruwa da dama na ga sun yi kaura,
Silar fadan gida ko ko fadan makara,
Dirshan garin Biu nan na gana bai da tsara,
Dabe na makuba ba za a banbare ba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
9
Can wanni lokaci da Jukun su kayyi daga,
Su ka turnuke gabas yaki fada da daga,
Da dauki- ba-dadi hadari dashen kuringa,
Mai Idris Alooma ya na cikin manuba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
10
Aka auna arziki aka gayyato mayaka,
Idris Alooma yay farga ya gyara tufka,
Zakakuren Biu ya kira su dora jinka,
Kun san garin Biu ba za a kai su kas ba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
11
Shekaru daruruwa jingim gami da rana,
Jamhuriyar ga kafin ma ta sami suna,
Akwai garin Biu bijimin gari da suna,
Karni na sha biyar kafuwarsa je ka duba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
12
Da in ka tashi tun a hagunka har wa dama,
Masarauta guda ta Songhai ce ta ke da dama,
Najeriya Mali da Nijar da Libiya can ma,
Lallai garin Biu bai zam tuwon tishe ba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
13
Bisa Fedarliyar Biu an tawo da nisa,
Don samuwar hakan karni na sha tara sa,
Aka gwamutse da Askira da Shani ba marusa,
Sai Biu taz zamo masarautarta ba da wai ba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
14
Sarakunan Biu ba mai hali na gwaza,
Adalci a shimfide dukka sun ka wanza,
Tsoro bai san su ba balle ka zo da izza,
Tun Yamtarawala Biu ba a je zubar ba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
15
Kyawun zubi na al'adun da za a nuna,
Najeriya ta na da kabilun da za a nuna,
Ashe wadansu na a garin Biu ubana,
Garin Biu akwai masana adab ku duba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
16
Gurbatuwar sauyi zamani bai kai su kas ba,
Dadin gushi akwai arzikin noma da riba,
Noman hatsi abinda ba ai a ko'ina ba,
Garin Biu kasar noma ba 'yar kadan ba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
17
Garin noman dawa masara, gyada da wake,
Noman shinkafa gero dankali a duke,
Ga Noman rogo gwaza ga auduga sun damke,
Manoma garin Biu ba su san zaman zugum ba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
18
Tsohon cinikki na-dauri noma abin a nuna,
Kasar noma garin Biu arziki da suna,
Kowa ya bar gida to za a bar shi rana,
Ga noma da kun ga ba za a sha wuya ba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
19
Wasu tsaunuka na hango masu kyau na duba,
Tsaunin Tilla ga na Marama mu je mu duba,
Dutsen Shani tsaunin Gwaram taya ni duba,
Tsaunin Zobi da Gashina ban gan su wani gari ba.
 'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
20
Tafkin Tilla ga kogin Hawul na kowa,
In akwai ruwa gari kwai arziki ga kowa,
Kasar garin Biu ta dangane ga kowa,
A garin Biu noman kifi ba zai wuya ba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
21
Tafki da koguna ba su san wuyar ruwa ba,
Madatsan ruwa ko dam rayuwa ba tai wuya ba,
To ga ma'adanai na daka bai ga gari ba,
Gari garin zuwa Biu ba garin baro ba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
22
Ga dala da tsaunuka Biu dausayin muhalli,
Bishiyu nau'i i'ka da itatuwan kabuli,
Tsiron ganye don amfani gari na asali,
Najeriya garin Biu ne tauraro na duba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
23
Fannin sarakuna ba a kai su jarumai ba,
Mulki da kambami da bajintaka ta duba,
Kuthlan garin Biu talakansu bai uhm ba,
Masu martaba tili a garin ga ba kadan ba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
24
Jagora:
Jerin sarakuna na Biu,
Tsarin sarakuna na garin,
Ga tsarin sarakuna na Biu,
'Yan Amshi:
Farfesan waka himma haka dai,
Ina batun sarakunan na Biu:
25
Tun zuwan Yamtarawala Kuthlin Biu na farko,
Sai Mari Virahyel Kuthlin Biun ga na biyu,
Kuthli Dirawala sarki na ukku a Biu,
Ga Yamta Amba shi ya rike Biu a na hudu,
Yamta Kupaya Wadi na biyar fagen sarakai,
Mari Watila Yamta na shidansu ba da wai ba,
Yamta-ra-Bangye ne na bakwai gwarzo a Kuthli,
Sai mu je ga Mari Luku na takwas dan Yamta Bangye,
Mari Jakwa Birtiktik ga Maza maki garje,
Mari Thlama Bahara gamji gwani a Kuthlai,
Na sha daya shi ne Mari Tayarwarinki dodo,
Kuthli Tayarwarinki na sha biyun mazaje,
Mari Kopchi ne ya dau Biu sha ukun sarakai,
Kuthli Diporma kun ji na sha hudunsu kenan,
Sai Garga Moda nas sha biyar ku bi ni sannu
Kuthli Dimoda sha shida kun ji dan sarakai,
Sai Kuthli Dibiya dan Kuthli Dimoda a biye,
Kuthli Dirawa Dibiya na sha takwas a jere,
Shi Garga Kwapchi sha tara ne in ka bi da kirga,
Mari Watirwa yana tafe shi ma mu sa shi man,
Na ashirin da dayya Ari Paskur Ari kenan,
Sai Mari Biya ashirin da biyu ka ji shi ma
Ga Garga Kwamting na ashirin da ukku kenan,
Mai Ari Dogo na ashirin da huddu Kuthli,
Mai Ari Gurgur yay gadon gadon sarautar,
Da shidda Mai Muhammadu Aliyu Mai Madu a,
Kuthli ashirin da bakwai Mai Mustafa Aliyu,
Kawo har zuwa Mai Umar Muastafa Aliyu,
A sarautar Biu na ashirin da takwas yaz zo
Garin Biu kunshin masarautarsa kwai nagarta,
26
Masarautar Biu ta kunshi garuruwa da dama,
Ga Bayo ga Biu hagu ke da tausa dama,
Kwaya Kusar Hawul masana ado da himma,
Najeriya ashe Biu ta dade da haiba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
27
Shi faskaren gwani hadda ke sa a wanke,
Da dan nutsa cikin bincike sai kai ya kuke,
Wannan gari akwai harsuna da za damke,
Bishiya guda ba tai dajin da ba ya shi ba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
28
Baburawa da Burawa manyan yare ne a Biu,
Terawa Kanakuri su ma akwai su a Biu,
Chibok na ce ga Marghi su ma akwai su a Biu,
Pidlindawa da Jarawa harsunan ga duba,
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
29
Komberawa da su a Biu ta rungume su,
Fulanin Kitaku yaki ba a ajje masu,
Fulanin Bararoji Biu ce ta zam gidansu,
Gagara gasa sai Biu ba garin zubar ba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
30
Wannan garin a je dubbai fadawa kowa,
Ba fariya ba ya fi gaban a zayyanawa,
Zaki sai zuma Biu warwarar abawa,
Wanne garin ka je? Ba ka je garin Biu ba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
31
Tumbatsar gari ya amsa gari ba wala-wala ba,
Fuskar salsalarsa ta cika ba sawarwari ba,
Tafki na tarjamar illimi ba fagen wasa ba,
Dr Bukar garin Biu ba shi ya da kai ba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
32
"A History of Biu" cikin harshen nasara,
Tarihin garin Dakta Bukar ya sara,
Dakta Bukara Usmanu mai farar dabara,
Mai kishin garin Biu sannu sannu baba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
33
Tarihi ya ke naudo jiya yau ta gane kanta,
Don yau ta hau bisa kadamin ganin gabanta,
Sirrin garuruwa da yawa ka ba su rata,
Littafin Bukar garin Biu bai rufe mu dai ba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
34
Tunkahon mutum ba zai wuce shi a kira sa shi ba,
Littafi guda da warka sitta mi'a duba,
Shafika dari shida ko dai ba da baddali ba,
Tarihin Biu Bukar yay wa taskira ta duba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
35
Ga kissa murucin dutse ga ji da gayya,
Biu ce tsiro tsiron da harden 'yan hamayya,
Mai neman fada dage ya gan ka kar ka buya,
Masu yakar garin Biu ba a kai su faduwa ba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
36
Wanna Dr Bukkari? Bukar Usman gwanina,
Gwanin mutan Biu da Nigeria ka zana,
Dakan Adab cikin Adabi ya na da gona,
Gonar Adab ba duk masani ya ke da ita ba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
37
Fadar garin Biu ba daga nan a ilimi ba,
Kwai wani rawani ba duk kai ya ke hawa ba,
Rawanin Dan Masani ko an sa kai ba shi karba,
Sai an gamon-katar rawanin bai batan gida ba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
38
Dan Massanin Biu ba rawanin gama gari ba,
Dan Massanin Biu ba zai auri kan rago ba,
Domin masu illimi sarautar take ta duba,
in babu illimi rawanin ma ba za shi hau ba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
39
Zumunci kishin gari ya kan dangana ga komai,
Mutunci kakan wuri shi ke sayewa komai,
Wanda ya kai tsayin tsayau tsayin karan tsawonsa kai mai,
Dan Masanin Biu Bukar Usman na duba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.
40
Dan Masanin Biu na kirawo uba gurina,
Mai illimi da binkice hidima dare da rana,
Cancantar Dan Masani Bukar Usman ta nunan,
Allah Kai mu lokacin nadi ba a yi babu mu ba.
'Yan Amshi:
Garin Biu aje dubbai fadawa kowa
Jagora:
ka zaga duniya ba ka je garin Biu ba
'Yan Amshi:
Farfesa ya ce ba ka zaga ko'ina ba.